1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Dakarun Amurka sun kammala fita

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 5, 2024

Amurka ta kammala janye baki danyan sojojinta daga sansaninta na karshe a Jamhuriyar Nijar, sama da shekara guda bayan sojoji sun karbe iko a kasar da ke yankin Yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4j8jk
Jamhuriyar Nijar | Agadez | Sojoji | Amurka
Tsohon sansanin sojojin Amurka na Air Base 201 a birnin Agadez na Jamhuriyar NijarHoto: Carley Petesch/AP Photo/picture alliance

Amurkan dai ta kammala janye baki danyan sojojin nata ne, bayan sojojin da suka karbe iko a Jamhuriyar ta Nijar sun bukaci ta kwashe ilahirin dakarunta daga kasarsu jim kadan bayan kifar da gwamnatin farar hula ta hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum. Ma'aikatar tsaron Amurkan Pentagon ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Jamhuriyar ta Nijar, inda ta ce  an kawo karshen janye dakarun Amurka daga sansanin sojojin samanta na Air Base 201 da ke birnin Agadez.