1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kammala janye sojojin Amurka daga Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
July 5, 2024

Kasar Amurka ta bayyana shirin kammala janye dakarunta daga Jamhuriyar Nijar, a ranar Lahadin da ke tafe. Nijar na da daya daga cikin manyan tashoshin kula da jiragen sama masu sarrafa kansu da kimanin dakaru 1,000.

https://p.dw.com/p/4hx6d
Nijar | Amurka  | Sojoji
Dakarun Amurka za su kammala fita daga NijarHoto: Carley Petesch/AP Photo/picture alliance

A watan Afrilun wannan shekara ta 2024 ne dai, gwamnatin juyin mulkin sojan Nijar ta bukaci Amurka ta janye dakarunta daga kasar da ke yankin yammacin Afirka. Gabanin juyin mulkin watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2023 a Jamhuriyar ta Nijar da ya kawo karshen gwamnatin Mohamed Bazoum dai, kasar ta kasance mai dasawa da Amurka da ma sauran kasashen Yammacin Duniya. Sai dai tuni wannan alaka da ke tsakanin Nijar din da kasashen Yamma ta zama tarihi, inda mahukuntan sojan suka karkata zuwa Rasha.