1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cutar Lassa ta billa a Jihar Kano

Nasir Salisu Zango GAT
January 21, 2020

Mahukunta a Jihar Kanon Najeriya sun tabbatar da mutuwar wasu likitoci biyu da wata mata daya a sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa, bayan da suka gudanar da gwaji a kan jinin mutanen.

https://p.dw.com/p/3Wc3K
Symbolbild Forschungsbeziehungen Deutschland Afrika
Hoto: picture-alliance/Ton Koene

Mahukunta a Jihar Kanon Najeriya sun tabbatar da cewar gwajin jini da aka gudanar na wasu likitoci biyu da wata marar lafiya da suka rasu, ya tabbatar da cewar an sami kwayoyin zazzabin Lassa a cikin jininsu, lamarin da ya tabbatar da barkewar zazzabin na Lassa a Jihar ta Kano.

Da farko dai an shiga rudanin a Jihar Kano bayan mutuwar mutanen uku, yayin da wasu kuma ma'aikatan jiyya da likita guda ke kwance a asibiti rai kwakwai mutu kwakkwai, sakamakon wani zazzabi da ake zargin zazzabin Lassa ne.
 
Shugaban asibitin koyarwa na Malam Aminu Farfesa Abba Sheshe ya bayyana cewar zuwa yanzu sun shiga fadakar da mutane, kan hanyoyin kauce wa wannan cuta. Sannan ya ce akwai sauran ma'aikatan lafiya da suka yi mu'ammala da wata marar lafiya da ake zargin ita ce ke dauke da cutar, dan haka suma an mika su cibiyar killace masu cuta dake garin Yar Gaya, kuma ana cigaba da nemo wadanda ake zargin sun shafi cutar domin killace su.