1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola na ci gaba da yaduwa

Mohammad Nasiru AwalDecember 26, 2014

Rashin taimako da ya dace daga kasashen duniya don magance bazuwar Ebola, shekara guda bayan bullarta a Afirka ta Yamma.

https://p.dw.com/p/1EAJ1
Liberia Monrovia Zentrum Deutsches Rotes Kreuz
Hoto: DW/J. Kanubah

Har yanzu dai cutar Ebola da ta addabi wasu kasashen yankin yammacin Afirka na ci gaba da daukar hankalin jaridun na Jamus. A wani labari mai taken kwayar cutar da ta yi barazana ga zabe, ana fuskantar dambarwar siyasa a Afirka ta Yamma saboda cutar Ebola, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi.

Har yanzu ba a maganar saukin lamarin. A karshen mako kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta bude sabuwar cibiyar kula da masu fama da Ebola a yammacin Afirka. Kungiyar likitocin na kula da cibiyoyin kula da marasa lafiya guda bakwai a cikin kasashe uku da Ebola ta fi shafa wato Laberiya da Guinea da kuma Saliyo. Shekara daya ke nan da kwayar cutar ta bulla a yankin, amma har yanzu ba a samu wani taimako na a zo a gani daga kasashen duniya ba. Tun ba yau ba masana tattalin arziki ke nuni da fuskantar mummunar karayar tattalin arziki sakamakon annobar. Amma kuma yanzu masu lura da lamura na fargaba game da dorewar kwanciyar hankalin siyasa a kasashen uku. Ebola na barazana ga tsaro da zaman lafiya a Laberiya da Saliyo da kuma Guinea.

Ita ma jaridar Neues Deutschland tsokaci ta yi game da cutar ta Ebola tana mai cewa a kasar Laberiya ana nuna wa yaran da iyayensu ke fama da Ebola wariya. Ta ce saboda tsoron harbuwa da kwayar cutar Ebola, yaran da iyayensu suka mutu sakamakon Ebola, na fuskantar tsangwama musamaman daga danginsu. Yanzu haka dai kungiyar agaji ta Children's Village ke kula da wadannan yara marayu a wasu kebabbun cibiyoyi na musamman.

Kawo karshen tsangawa ga matai da ake zargi da maita

Bildergalerie Kenia Zwangsheirat Dezember 2014
Hoto: Reuters/S. Modola

Har yanzu dai muna kan batun tsangwama amma wannan karo a kan tsofaffi da ake zargi da maita a arewacin kasar Ghana. A labarin da ta buga game da batun jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi gwamnatin Ghana ta fara daukar matakan kawo karshen wannan al'ada ta dora wa tsofaffi laifin maita.

Ta ce gwamnati ta rufe wasu sansanoni da ke zama mafaka ga wadannan tsofaffin da ake zargi da maita, kuma yanzu haka an dauki matakan sake shigar da su cikin al'umma. Jaridar ta ce matsalolin talauci da rashin gata da kuma jahilci ke sa ake tsangwamar wadannan tsofaffi wasu lokutan ma har da ‘ya'ya da jikokinsu, inda suka gudu zuwa sansanonin mayu don kaucewa kisa. An yi kiyasin cewa mata fiye da 1000 ne suka kwashe shekaru gommai a irin wadannan sansani cikin wani mawuyacin hali na rashin samun kulawa da ta dace. Amma yanzu gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu sun tashi haikan don kawo karshen wannan da daddiyar al'ada.

Rikicin Boko Haram ya zama gagarabadau

Ita kuwa jaridar Die Zeit hankali ta mayar a kan rikicin Boko Haram a Najeriya tana mai cewa kungiyar ta zame wa hukumomin kasar gagarabadau. Ta ce a kullum mayakan kungiyar na kai hare-hare a kan wadanda ba su ba su gani ba. Inda kwanaki kalilan gabanin bukukuwa kirsmetti kungiyar ta tsananta aikace-aikacenta a kan mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya. A wata hira da ta yi Archbishop Ignatius Kaigama na garin Jos, jaridar ta rawaito shi yana cewa rikicin na Boko Haram da ke nasaba da siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewa, rikice ne mai daure kai, wanda alhakin kawo karshensa ya rataya wuyan shugabannin siyasa.