1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin COVID-19 ga Almajirai a Najeriya

April 24, 2020

Gwamnatocin yankin arewacin Najeriya, sun fara mayar da yaran da aka kai almajiranci jihohinsu zuwa garuruwansu na asali, da nufin sada su da iyayensu domin kare su daga kamuwa da cutar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3bNXb
Nigeria Katsina | Coronakrise | Almajiri Vertreibung
Matakin mayar da Almajirai jihohinsu na asali a NajeriyaHoto: DW/Y. I. Jargaba

Daga cikin jihohin da ke kan gaba wajaen mayar da Almajiran garuruwansu na asali dai akwai jihar Kano, inda tuni ta mayar da wasu Almajirai zuwa jihohin Jigawa da Katsina. Gwamnatin jihar ta Katsina dai, ta karbi yara Almajirai 'yan asalin jiharta daga jihar Kanon har guda 419. Bayan da likitoci suka yi wa Almajiran gwaje-gwaje dan tabbatar da lafiyarsu, daga nan ne kuma aka dauke su zuwa kananan hukumomin nasu kafin aga bisani a mika su ga iyayensu tare da bukatar su killacesu na tsawon makonni biyu.

Inganta makarantun allo

A cewar Dr Abba Bashir Dankyallori shugaban sashin nazarin da dab'i kan Al-Qur'ani na jami'ar jihar Yobe, wanda shi ma ya ce ya yi almajiranci kuma ya yi karatun zamani, ya zama dole gwamnati ta tsayawa al'majiran yadda take kulawa da sauran daliban makarantu na zamani.

Tuni dai gwamnatocin jihohin Kaduna da Gombe da Kano su ka fara mika wadannan yara, lamarin da Sharif Bashir Abul-Fathi ya ce ba alheri ba ne. Sai dai jami'an kiwon lafiya na ganin daukar matakin da gwamnatocin jihohin arewacin Najeriyar ke yi na mayar da Almajiran zuwa jahohinsu, abu ne da ya zama wajibi domin kare lafiyarsu da ma ta sauran al'umma. Mustapha Muhammad Inuwa shi ne sakataren gwamnatin jihar Katsina, kuma ya ce da ma kafin mahukuntan Kanon su mika masu Almajiran sai da suka killacesu tsawon mako guda. Ya kuma ja ya ja hankalin iyaye da su guji tura yaransu makarantun allo dan kare lafiya da kuma tarbiyyarsu.
A hannu guda kuma, masu rajin kare hakkin mata da yara na bayyana damuwa kan makomar yara Almajirai da sauran yara marayu da ba su san halin da su ke ciki ba, a daidai lokacin da cutar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa a sassan Najeriya. Irin wadannan yara dai ya zama dole su fita su nemi abin da za su ci, duk da cewa akwai makarantun allo da suka killace nasu almajiran suna ciyar da su ba tare da sun fita bara ba.

Symbolbild Hände waschen
Bukatar kula da tsaftaHoto: Imago Images/M. Westermann
Die Bettel-Schüler aus Nordnigeria
Inganta makarantun alloHoto: DW

Tallafi ga Almajirai

Haka kuma babbar damuwa kamar yadda masu kare hakkin yara a jihar Borno da aka fi kai Almajiran karatu, kamar Malama Hadiza Abubakar suke bayyanawa shi ne ba sa samun fadakarwar da ake yi wa yaran balle su dauki matakai na kare kawunansu, inda suke shiga wurare suna taba abubuwa kuma su ci abinci ba tare da wanke hannuwansu ba. Yanzu haka dai wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun fara kokarin taimakawa wadannan yara, sai dai masana na ganin kamata ya yi a kai taimakon har makarantunsu.