1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: An gurfanar da mutane 149 a Legas

Ahmed Salisu
April 17, 2020

Rundunar 'yan sandan jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta gurfanar da mutane 142 gaban kuliya saboda keta dokar hana fita da aka sanya a jihar a wani mataki na rage karuwar masu dauke da cutar nan ta Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3b4Ma
Nigeria Homosexualität Polizei-Razzia in Lagos
Hoto: Reuters/T. Adelaja

Wata sanarwa da rundunar 'yan sanda Legas din ta fidda wadda ke dauke da sa hannun kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi, ta ce wadanda aka gurfanar din sun aikata laifukan da suka hada da kisan kai da fashi da makami da kuma fita kan tutina don yin harkokinsu duk kuwa da dokar hana fita da aka kafa.

Tuni dai kotu ta bada umarnin tsare mutanen a wajen 'yan sanda har zuwa wani lokaci nan gaba inda kotun za ta sake zama ta cigaba da sauraron karar da aka gabatar.

Jihar Legas dai ita ce kan gaba a yawan mutanen da ke dauke da cutar ta Covid-19 kuma tun bayan da aka sanar da sanya dokar hana fita, mazauna birnin suke korafi na karuwar aikata manyan laifuka.