1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Badakalar cin hanci a fannin tsaro

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 28, 2018

Kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ce ta gano zargin badakalar cin hanci a makudan kudin da ake ware wa da sunan harkar tsaro a Najeriya wato "Security Votes".

https://p.dw.com/p/2ySfK
Nigeria Plakate und Aufkleber gegen Korruption
Hoto: DW/K. Gänsler

Kungiyar ta Transparency International da ta kaddamar da rahoto kan wani bincike da ta gudanar mai zurfi ta ce ta bankado zargin tafka cin hanci da rashawa a makudan kudin da ake ware wa fannin tsaro a Najeriyar da yawansu ya kai sama da Naira bilyan 241 a kowace shekara, kuma abin karuwa yake. Kungiyar ta ce almundahanar ana yin ta ne kama daga matakin gwamnatin tarayya zuwa jihohi, domin kuwa a cewarta rahoton ya gano cewa jihohi 29 na Najeriya sun gaza bayanin yadda suka kashe dalar Amirka miliyan 580 da suka karba da sunan harkokin tsaro a shekara guda. Rahoton ya kuma gano yadda ake karkatar da wadannan kudade ta hanyar yakin neman zabe, sannan ana zargin jami'an gwamnati na zuba sauran a aljihunsu.

Nigeria UN Camp in Maiduguri
Rashin tsaro ya tilasta dubban mutane tserewa daga gidajensu a NajeriyaHoto: picture alliance/dpa/AP/S. Alamba

Karkatar da kudin zuwa ma'aikatun da ba su da alaka da tsaro

Abin da ya fi daga hankali a rahoton shi ne yadda wasu hukumomin da basu da alaka da tsaro a Najeriyar ke karbara wadannan kudade a yanayi na a bi yarima a sha kida, biyu daga ciki da aka, ambato su ne hukumar kula da harkokin yawan bude idanu da makarantar koyon aikin hakora. A binciken nasu sun gano cewa an samu karuwar wadannan kudade da akan kebe a shekarar 2017 da ta gabata da ma kasafin kudin wannan shekara, bayan kuwa an samu raguwar su a farkon shekara ta 2016 a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. A ta bakin Katherine Aitken mai ba da shawara a fannin tsaro ga kasashen Afrika da ke ofishin jakadancin Birtaniya wannan rahoto muhimmin ci gaba ne na binciken da aka yi a kan yadda ake tafiyar da kudaden sashin tsaro a Najeriya da suka zama wata kafa ta tafka cin hanci da rashawa a dai-dai lokacin da Najeriyar ke fuskantar kalubale a sashin tsaron, ta kuma yi fatan cewa binciken zai samar da wata kafa ta gudanar da sauye-sauye da zai samar da kyakkyawar makoma. Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ta bakin wakilinsa ya ce za su yi nazari a kan wannan rahoto domin majalisar ta dauki matakin da ya dace.