1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cikakken bayani game da cutar mashako

Suleiman Babayo MAB
July 31, 2023

Daruruwan mutane sun kamu da cutar mashako ko diphteria a fadin Nigeria, inda aka tabbatar cewa jihar Kano ce ta zama a kan gaba a cikin jihohi masu hadari a yanzu. Wane rukunin mutane take kamuwa da ita?

https://p.dw.com/p/4Ub9C
Kwayar cutar da ke haddasa mashako wato diphteriaHoto: picture-alliance/OKAPIA KG/G. Gaugler

Mutane akalla 80 ne alkaluma suka nuna cewar sun rasa ransu a dalilin wannan cuta ta diphteria a fadin Nigeria. Sai dai hukumomi na kokarin ganin sun shawo kan yaduwarta. Daruruwan mutane sun kamu da cutar mashako a fadin Nigeria, inda aka tabbatar cewa jihar Kano ce ta zama a kan gaba a cikin jihohi masu hadari a yanzu.  shin mine ne cutar Mashako wato Diphtheria? Wane rukunin mutane take kamuwa da ita? Dr. Bala Gadanga na asibitin Jami'ar Usmanu Dan fodiyo da ke Sokoto ya yi karin bayani.