1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChaina

Chaina da Philiphines sun daidaita kan tsibirin Thomas Shoal

July 22, 2024

Kasashen biyu sun shafe shekaru suna takaddama kan tsibirin na Thomas Shoal da ke kudancin tekun Chaina.

https://p.dw.com/p/4iZbB
Tsibirin Thomas Shoal
Tsibirin Thomas ShoalHoto: Adrian Portugal/REUTERS

Kasashen Chainada Philiphines sun sanar da cimma yarjejeniya don kawo karshen takaddama da suke yi a kan wani tsibiri dake kudancin tekun Chaina, ba tare da bayyana  abin da aka cimma ba. Dukkan kasashen biyu na ikirarin mallakar tsibirin na Thomas Shoal wanda ke karkashin ikon fadar mulki ta Manilan a yanzu.

Karin bayani:Amurka da Pilippines na atisayen soji a tekun kudancin China

Philiphines ta kafa wani jirgin ruwa a shekarar 1999 domin sake nuna karfi da kuma ikonta akan tsibirin, ta kuma aike da wasu kananan jiragen ruwa a yankin. Sai dai Jiragen Chaina na amfani da wasu bututai masu fesa ruwa domin hana jiragen Philiphines samun damar zirga-zirga a yankin.

Karin bayani: EU na duba yiwuwar rage wa Chaina harajin shigar da motocinta Turai

An yi ta nuna damuwa kan karuwar zaman dar-dar a tsibirin da kuma yiwuwar tsoma bakin Amurka. Philippines ta na da dangantakar soji da Amurka kuma a na ganin za ta iya mara mata baya akan Chaina.