1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa mai karfi ta halaka mutum 5 a Chaina

July 6, 2024

Mutum biyar sun mutu a Chaina yayin da wasu 83 suka jikkata sakamakon wata guguwa mai karfi da ta doshi kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/4hxpq
Guguwa mai karfi ta halaka mutum 5 a China
Guguwa mai karfi ta halaka mutum 5 a ChinaHoto: Deng Hua/Xinhua/AP/picture alliance

Rahotanni daga Chaina sun tabbatar da mutuwar mutum biyar yayin da wasu 83 suka jikkata sakamakon wata guguwa mai karfi da ta doshi gabashin lardin Shandong. Tun dai a ranar Juma'a ne guguwar ta fara kadawa a birnin Heze.

Hukumomi na cewa, kimanin gidane dubu uku ne da layukan wutar lantarki 48 da kuma gonakai da suka kai fadin hecta dubu hudu ne suka lalace sakamakon iftila'in. Hukumar kula da hasashen yanayi ta China ta ce, daman an saba fuskantar makamancin wannan iftila'in a wasu lardunan da ke kudancin kasar.