1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ceto yara tara da aka sace a Kano

Gazali Abdou Tasawa
October 15, 2019

A Najeriya batun yaran nan 'yan asalin jihar Kano da aka sata aka kaisu jihar Anambra da ma sauya musu suna na ci gaba da kawo rudani a kasar bayan da iyayan yaran da aka sace suka ce adadin yaran ya kai 47.

https://p.dw.com/p/3RKks
Bettelnde Kinder in Dutse, Nigeria
Mun yi amfani da tsohon hoto ne kawai.Hoto: DW/Z. Rabo Ringim

Yara tara ne aka gano a birnin Onitsha bayan da aka kama wani mai suna Paul yana kokarin daukar wani yaro domin fita da shi. Sai dai kuma daga bisani iyayen yaran sun ce adadin yaran da aka satar musu ya kai 47. A kan haka ne suka yi kira ga 'yan sanda kan su tsananta bincike domin gano sauran yaran.

Tun karshen makon da ya gabata ne dandanlin sada zumunta musmaman ma na facebook da twitter suka tumbatsa da labarin gano kananan yara tara da ake zargin an sace su daga unguwanninsu da ke Kano sannan aka yi safarar su zuwa kudancin kasar, kafin daga baya aka sauya musu suna aka kuma sayar da su. To amma daga bisani iyayen yaran sun bayyana cewar ba wai yara taran nan ne kadai fa aka sace ba ,domin tun a baya sun tantance sunayen yaran da aka sata su kimanin 47, dan haka suke rokon mahukunta da su taimaka a ci gaba da bincike domin bankado ragowar wadanda aka sace. 

Nigeria UN Camp in Maiduguri
Mun yi amfani da tsohon hoto ne kawaiHoto: imago/epd/A. Staeritz


Hedikwatar 'yan sanda da ke Bompai ta cika makil da iyayen yaran da aka sata, inda wadansu suka yi dace 'ya'yansu na cikin tara da aka gano, yayin da wasu kuma wannan abu ya zame musu tamkar wani fata na samun nasu 'ya'yan a nan gaba

A cikin watan Aprilun da ya gabata dai wata babbar kotu a Kano ta yi hukuncin daurin shekara 10 ga wata 'yar kabilar Igbo mai suna Love Oga bisa samunta da laifin satar yara. Haka kuma wata kotun kananan yara karkashin mai sharia Salma dan Baffa ta aike da wasu almajirai zuwa gidan gyaran hali bayan samunsu da laifin satar yara suna kai wa wasu mata ana ba su ladan Naira dubu daya kowane yaro.