1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce kan yawon Shugaba Tinubu

August 21, 2024

A yayin da ake kallon karuwar kai-kawo na shugabannin Tarayyar Najeriya zuwa kasashen waje, ana dada nuna alamun damuwa cikin kasar da ke fadin babu kudin tafi da harkokin ci-gaban al'umma.

https://p.dw.com/p/4jkuv
Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Yawo | Tsadar Rayuwa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sodiq Adelakun/AFP

Tun dai ana karatun hujja, sannu a hankali bakunan masu mulkin Najeriyar na kara shiru a kan kai-kawon shugabannin kasar zuwa waje. Ga misali dai shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu na birnin Paris, ba kuma tare da 'yan kasar sun san hujja ba. Kuma kama daga watan Fabarairu na shekarar bana zuwa watan Yuli na jiya dai, Najeriyar ta batar da dubban miliyoyin Naira da sunan zirga-zirgar shugaban kasar da mataimakinsa. Wata kungiyar da ke bin diddigin yadda ake kisan kudin gwamnatin kasar ga misali ta ce an sayi dalar Amurka miliyan daya da dubu 200, domin wata ziyara ta shugaban kasar zuwa Dubai kadai a watan Fabarairun bana. Cibiyar dai ta kuma ce a tsakanin ranar 24 ga watan Fabarairun ya zuwa 14 na Maris na banan dai, kasar ta kashe Naira miliyan dubu biyu da 900 domin sayen kudin kasashen waje ga shugaban da mataimakinsa yayin tafiyarsu zuwa kasashen Habasha da Switzerland da Faransa da Laberiya da ma kasar Cote d'voire. Kisan kudin kuma da yanzu haka ke jawo dagun hakarkari cikin kasar dake fadin babu kudi.

Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Yawo | Tsadar Rayuwa | Zanga-Zanga
Ba da jimawa ba ne dai, al'ummar Najeriya suka yi zanga-zangar neman sauyiHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Yunusa Tanko dai na zaman kakakin jam'iyyar Labour da ke adawa, kuma ya ce kai-kawon shugaban na kama da kokarin sharholiya cikin kasar da masu mulkin ke kiran karatun hakuri. Sharholiya da dukiyar al'umma ko kuma kokari na sauya rayuwa, ana dai dora hujjar neman jari na waje da kokarin sauya tunani a kan kasar cikin hujjar kai-kawon na shugabanninta. Kai-kawon kuma da a cewar Abdullahi Tanko Yakasai da ke bai wa shugaban kasar shawara cikin harkokin al'umma, ta fara nuna alamun nasara cikin kasar a lokaci kankane. Kama daga birnin Paris da ke zaman kasa ta biyu ta shugaban ya zuwa birnin London, sau dai-dai har 17 ne dai Tinubun ya sa kafa ya bar Najeriya a shekara guda ta mulkin nasa. Kuma duk da cewar dai ba ya zama na kan gaba cikin shugabannin kasar da suka kafa tarihi cikin batun kai-kawon, Tinubun dai na ziyarar tasa ne cikin yanayi maras kyau da Najeriyar ke fama. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin harkar mulki, kuma ya ce kai-kawon masu mulkin kasar na zaman tunanin 'yan bokonta da babu ranar sauya shi. Tarayyar Najeriyar dai daga dukkan alamu na tsakanin bude ido da kila aiki tukuru, a kokari na gyara ga kasa da kuma rufe idanu a cikin sababbin jirage kan hanyar kai wa ga jarin na waje.