1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece kuce kan kundin tsarin mulkin Najeriya

Uwais Abubakar IdrisApril 16, 2015

Takaddma ta kunno kai bayan da shugaban kasa mai barin gado Goodluck Jonathan ya ki sanya hannu kan gyaran da aka yi wa tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/1F9Vi
Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan in Brüssels
Hoto: picture-alliance/dpa

Shekaru uku da rabi 'yan majalisar dokokin kasar suka kwashe suna aikin sake fasalin tsarin mulkin Najeriyar, abin da ya kai ga gudanar da tarurrukan jin ra'ayoyin jama'a a mazabun tarayya har 360, baya ga wanda majalisun dokokin jihohin kasar 36 suka yi. Amma duka bayan bata wannan lokaci da ma kudi shugaba Goodluck Jonathann da aka aika mashi don sa hannunsa, ya yi kememe a kan lamarin.

Aikawa da wasika ga 'yan majalisar da shugaban ya yi na neman a sake gyara wasu sassan ya sanya 'yan majalisar fusata a kan matakin da shugaba Jonathan din ya dauka. Sanata Abdul Ningi dan jam'iyyar PDP ne a majalisar dattawan Najeriyar.

"Abubuawan da muka ji aka karanta a gaskiya ya ba mu takaici kuma ya ba mu dariya don ba maganar Jonathan ake ba, ana maganar kowane shugaban kasa ne da ya shigo. Munga karfin ikonsa ya yi yawa a wannan kasar, kusan shi ne wuka shi ne nama. To ba da Jonathan muke ba, muna magana ne da duk wani shugaban kasa ne da ya zo ya san cewa mutane su ake wa mulki, kuma ra'ayin jama'a aka tambaya har aka yi wadannan gyare-gyare."

Shugaba Jonathan ya zarta huruminsa

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Ginin majalisar dokokin Najeriya a AbujaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Shugaba Jonathan dai ya yi korafi ne a kan cewar wasu daga cikin gyare-gyren ba su yi mashi dadi ba, musamman batun rabe ofishin ministan shari'a da na Attorney-janar zuwa gida biyu, da karbe ikon sanya hannu a kan kudurin doka da 'yan majalisar suka yi. Abin da ya sanya Sanata Ita Enang na jam'iyyar adawa ta APC bayyana cewa shugaban fa ya zarta huruminsa.

"Karara a fili na bayyana cewa shugaban kasa ba ya da ikon ya rubuto mana abin da ya yi a yanzu a kan wannan batu, domin wannan ai abubuwa ne da ya kamata a ce ya yi kai tsaye, ko ta hannun Attorney-janar ko wakilinsa a majalisa a lokacin da ake sauraren jin ra'ayi jama'a. Amma bayan 'yan Najeriya sun ba da gudumawarsu, da ma sauran jama'a, sa hannun mutum guda ba zai lalata abin da daukacin 'yan Najeriya suka yi ba."

Murna ta koma ciki ke nan?

Nigeria Karu Wahlen Wähler
'Yan Najeriya na fatan ganin an yi wa tsarin mulkin kasar gyare-gyareHoto: DW/Scholz/Kriesch

Ganin takaddamma da ma rudanin da wannan mataki ya haifar ga daukacin aikin gyaran tsarin mulkin Najeriyar da al'ummar kasar suka dade suna sa rai da fata a kansa. Duk da dakile wasu muhimman sassan da suka so ganin an samu canji na bai wa kanana hukumomin 'yanci cin gashin kansu, ko mece ce mafita a yanzu? Barrister Mainasara Umar lauya ne da ya kware a fanin dokokin tsarin mulki.

"Wannan ba wani abu ba ne na matsala ba domin sashin tsarin mulki na jamhuriyar Najeriya sashi na 57 sakin layi na 4 ya bai wa shugaban Najeriya iko na kwanaki 30 ya sa hannu ko ya ki sa hannu a duk wani kuduri na doka. In ya ki sa hannu ko kuma ya ce bai amimce ba, dai-dai yake da yaki sa hannu. 'Yan majalisa sai su dawo su yi amfani da sashi na 57 sakin sashi na 4 wanda ya ce 'yan majalisar dokoki za su nemi kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar, su taru su amince da doka. Da zarar sun yi haka ta zama doka ba sai shugaban kasa ya sa hannu ba."

Da alamun aikin gyaran tsarin mulki a yanzu ya kai matsayi na rijiya ta bayar guga ta hana. Abin jira a gani shi ne ko a wannan karon 'yan majalisar za su yi ta maza su yi amfani da karfin ikonsu wajen amincewa da kudirin dokar gyare-gyaren da suka yi wa tsarin mulkin Najeriyar.