Najeriya: Hada yara da manya a kurkuku
November 20, 2024Wannan matsala dai ta dade ana kuka da ita musamman ma idan aka duba yanayin da yaran da aka kama tare da tuhumar su da daga tutar Rasha yayin zanga-zangar yaki da yunwa da aka yi a Najeriyar, wannan ne ya kara motsa zukatan mutane har ma hankali ya koma kan irin wadannan yara da ba su kai munzalin balaga ba da ake kai wa ana gwamutsa su da rikakkun masu laifi lamarin da ke barazana ga rayuwar yaran da kuma daga hankulan iyaye da ma al'umma. Kwamared A.A AYAGI shi ne jagoran hadin kan kungiyoyi masu zaman kansu a Kano guda daga cikin hadakar kungiyoyin kishin al'umma da ke faftuka kan wannan matsala, a cewarsa abin yana ci musu tuwo a kwarya domin su ganau ne ba jiyau ba.
Barista Aisha Isa Yusuf lauya ce mai kishin al'umma da ke aiki a kungiyar PWAN wato Partners West Africa a Kano, ta bayyana cewar doka ba ta amince da wannan muzgunawa da ake yi wa yaran ba. To amma a martaninta kan wannan zarge-zarge Hukumar Kula da Gidajen Tarbiyya da Gyaran Hali ta jihar Kano ta bayyana cewa, ba ita ce ta kar zomon ba rataya kawai aka ba ta. Mai Magana da yawun hukumar a Kano SC Musbahu Lawal Kofar Nasarawa ya ce, alkalai ne suke kawo yaran su ajiyewa kawai suke. Yanzu haka dai kungiyoyin kishin al'umma da kungiyar Transperancy International, sun tashi haikan domin dakile wannan matsalar.