1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suka kan juyin mulki a Burkina Faso

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 27, 2022

Juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Burkina Faso, na shan suka daga al'ummomi da kungiyoyi na kasa da kasa. Ko ya makomar kasashen Afirka za ta kasance?

https://p.dw.com/p/46CgQ
Burkina Faso | Sabuwar gwamnatin juyin mulki
Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a kasar Burkina FasoHoto: Radio Télévision du Burkina/AFP

Da ma dai al'ummar kasar ta Burkina Faso, sun jima suna zanga-zangar adawa da matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar. Zanga-zangar da ta kwashi tsawoan lokaci, har ma ta kai ga sojoji sun yi wa Shugaba Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Fason juyin mulki. Juyin mulkin soja dai, kan sanya a kakaba takunkumi ga kasar da suka kwace iko da ita, sai dai hakan ba ya hana sojojin wata kasa yin juyin mulkin.

Babban kalubalen da a yanzu haka ke fuskantar kasashen Afirka musamman na yankin Sahel dai, shi ne matsalar rashin tsaro da ta'addanci, inda kuma a baya-bayan nan sannu a hankali sojoji ke yin juyin mulki. Ko da a kasar Mali ma dai, sau biyu ne sojoji suka yiu juyin mulki cikin shekara guda, abin da ya janyo kakabawa kasar jerin takunkuman karya tattalin arziki.