1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana Allah wadai da juyin mulkin Burkina

Abdullahi Tanko Bala MAB
January 25, 2022

Sojoji sun tabbatar da karbe ragamar mulkin kasar Burkina Faso, inda suka ce an hambarar da gwamnatin, sannan a rusa majalisar dokoki. Amma Amirka da kungiyar tarayyar Turai da kuma ECOWAS suka yi tir da juyin mulkin.

https://p.dw.com/p/463Uh
 Burkina Faso | Sojoji sun karbe mulki
Sojin Burkina Faso sun yi bore da ya kai ga hambarar da gwamnatiHoto: AP/picture alliance

Mutane a Burkina Faso sun wayi gari da sabuwar gwamnati karkashin mulkin soji bayan da ta sanar da hambarar da gwamnatin zababben shugaba Roch Marc Christian Kabore.

Tsawon kwanaki da aka shafe na boren sojoji da harbe-harben bindiga da ya jefa al'umma cikin halin rashin tabbas a Ouagadougou babban birnin Burkina Faso, ya kawo karshe da yammacin Litinin lokacin da wani ayarin sojoji ya bayyana a gidan talabijin ya sanar da cewa a yanzu gwamnatin na karkashin jagorancin kungiyar kishi da kariya da maido da martabar kasar.

A jawabinsa Jagoran tawagar Kaptin Sisdoré Kaber Ouedraogo ya ce yau "an shiga sabon babi a Burkina Faso, karni da kowane dan kasa ke da cikakkiyar dama da dinke baraka da hadin kai da zama tsintsiya madaurinki daya ,sannan da tabbatar da abin da ya hada mu baki daya wato martaba da 'yancinmu na y'an kasa."

Burkina Faso | Murna da juyin mulki
'Yan Burkina Faso sun yi murna da juyin mulkin Hoto: OLYMPIA DE MAISMONT/AFP/Getty Images

Mutane da dama a babban birnin kasar sun yi murna da juyin mulkin inda suka bazama kan tituna suna shaukin murna. Wani dan Burkina Faso ya ce "Dama na san za a rina, saboda gwamnatin ta gaza magance halin da aka shiga a Burkina Faso. Katse kafofin sadarwar Intanet ya kara dagula lamura yayin da mutane suke zaune ba tare da intanet ba."

Sojojn sun rufe dukkan iyakoki da sanya dokar takaita zirga-zirga tare da jingine kundin tsarin mulkin kasar. Sai dai ba su bayyana ko zuwa wane lokaci ne za su sake mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya ba.

Juyin mulkin dai na zuwa ne bayan watanni jama'a na nuna kosawa da gwamnatin Kabore na kasa shawo kan mayaka masu ikrarin jihadi da suka daidaita kasar kamar yadda wannan mutumin dan kasar ta Burkina Faso yake cewa: Ya ce "Idan kana mulkin jama'a akwai bukatar ka saurare su. Jawabin mai magana da yawun gwamnati a baya-bayan nan mai yiwuwa ya kara harzuka jama'a, a lokacin da ya ce ba dole ne gwamnati ta yi wa jama'a bayani ba. Dole ne, tilas gwamnati tana da hakki ta fito ta yi wa mutanen da suka zabe ta bayani."

Sai dai wasu 'yan kasar masu rajin ci gababn dimukuradiyya na cewa juyin mulkin soji babban komabaya ne ga dimukuradiyya a Afirka. Aziz Dabo wani kwararre kan sha'anin siyasa ya ce : "Muna cikin mawuyacin hali. A koda yaushe aka yi juyin mulki, komabaya ne ga dimukuradiyya saboda komai da ya shafi tsarin dimukuradiyya zai tsaya cik".

Tutocin mambobin AU
Tutocin mambobin kungiyar Tarayyar Afirka na kadawa a gaban cibiyar AUHoto: picture-alliance/landov

A waje guda dai shugabanin Afirka da na gamayyar kasa da kasa sun yi Allah wadai da juyin mulkin sojin inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga sojojin su gaggauta sakin shugaba Kabore da manyan jami'ansa da suke tsare da su. Ita ma hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wajibi ne a kare martabar dimukuradiyya a yammacin Afirka da kuma tabbatar da doka da oda.

A martaninsa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da juyin mulkin. A halin da ake ciki kungiyar raya ci gaban kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta bukaci sojojin su koma barikokinsu tare da bukatar tattaunawa da hukumomi domin sasantawa.