1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC na cigaba da asarar 'ya'yanta

Zainab Mohammed Abubakar
July 31, 2018

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/32PBu
Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Saraki ya bayyana ficewarsa daga APC din ne a wani sako da ya sanya a shafinsa na Twitter. Hakan kuwa na zuwa ne watanni kalilan gabannin babban zaben kasar wanda shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ke neman wani sabon wa'adin mulki. Sanata Saraki, wanda shi ne mutum na uku da ke da karfin iko a mulkin Najeriyar wani jigo ne a jam'iyyar ta APC. A makon jiya ne dai wasu 'yan majalisar dattawa 16 suka sanar da ficewa daga APC din, yayin da wasu 'yan majalisar wakilai 32 su ma suka yi sallama jam'iyyar.