1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zanga-zanga kan dokar zabe

Uwais Abubakar Idris
May 19, 2021

Gamaiyyar kungiyoyin farar hula sun gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin Najeriya, tare da niyyar ci gaba da zaman dirshin domin matsin lamba ga majalisar ta hanzarta kammala gyaran fuska a kan dokar zabe.

https://p.dw.com/p/3tczb
Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Kungiyoyin farar hular na Najeriya dai sun dauki wannan matakin ne biyo bayan jinkirin da ake fuskanta, abin da suke koken zai hana kyautata yanayin zabe a kasar. Kungiyoyin da ke rajin kare dimukuradiyya, sun rinka rera takensu a gaban majalisar dokokin Najeriyar, a wani mataki na nuna kin amincewarsu da jinkirin da ake samu. An dai yi wa wannan gyara karatu na daya da na biyu, inda har an kai ga gudanar da sauraron ra'ayin jama'a, amma daga nan aka ji shiru tamkar an shuka dusa. Sai dai har ya zuwa lokacin da wakilinmu ya hada wannan rahoton dai, babu wani jami'in majalisa da ya fito domin tarbar masu zanga-zangar.

Karin Bayani:'Yan majalisa sun karbi takardun samun nasara

Majalisar dai ta sha yin ikirarin cewa za ta kammala aiki domin amincewa da wannan doka, wadda sassan da ake fatan yi musu gyaran fuska suka hada da batun jefa kuri'a ta hanyar amfani da na'urar computer da ma tattara sakamakon zaben kansa, da yiwuwar bai wa 'yan Najeriya da ke kasashen waje damar yin zabe a duk inda suke, wadanda ke cikin matakan da za su taimaka wajen gudanar da tsaftataccen zabe, a kokari na kawar ko rage magudi.

Weltspiegel 22.02.2021 | Niger | Präsidentschaftswahl | Wahllokal
Fatan kammala gyaran dokokin zabe a Najeriya, gabanin zaben 2023Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Mr Ariyo Dare Atoye na  cikin masu wannan fafautuka: "Wannan ne kudurin dokar da aka fi so da daukar hankali a yanzu a Najeriya, saboda haka ne yasa muke tambayar me yasa 'yan majalisar nan ba sa son bin sahun bukatar 'yan Najeriya wajen kammala gyara wannan doka da za ta karfafa mana dimukuradiyya? Domin shiri ne na zaben 2023. Abin da za a sa a gaba bayan wa'adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari shi ne a zabi shugabanin na gari, gyaran fuska ga dokar zabe zai  bayar da damar zaben shugabanni na gari."

Karin Bayani: Rudani kan kudin shirya zaben Najeriya

Daga hankali da nuna dan yatsa ya biyo bayan daga lokacin kammala wannan aiki, domin sau biyu 'yan majalisar na sanya rana, amma kuma ake jin shiru, farko a watan Disambar bara da kuma watan Maris na wannan shekara. Desmond Joyce shugabar kungiyar NATU ta ce dokar za ta taimaka wa mata da ke harkar siyasa a Najeriya: "Idan aka amince da sabuwar dokar zabe da za ta bayar da damar tattara sakamon zabe ta hanyar na'ura, babu dalilin da zauna gari banza za su je domin kwace akwatin zabe, domin haka a amince da wannan doka da za ta bayar da damar shigar kowa a harkar zabe musamman mata, kashi shida ne kadai na mata a harkar siyasa a  daukacin kasar."