1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar gudanar da bincike a kan gyaran matatun man Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
June 1, 2023

A Najeriya, sama da tiriliyan 11 ne aka kashe a tsawon shekaru 10 da nufin gyara matatun man kasar 3, a cewar wani rahoton da majalisar dokokin kasar ta fidda, wanda kuma ta bukaci a zurfafa bincike a kai.

https://p.dw.com/p/4S4Jt
Nigeria I Hon Femi Gbajabiamila und Hon Kingsford Alban Bagbin
Hoto: Office of the speaker/Nigerian Parliament

Majalisar wakilan ta ce duk da wadannan makudan kudade da aka ware domin gyara matatun main kasar da ke tace kasa da kaso 30 cikin dari na man da ake amfani da shi, matakin da ya saka kasar dogaro da tattacen mai da ake shigo da shi daga kasashen waje, wanda da taimakon tallafin da ke kanshi ke rage tsadarsa.

Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da batu na janye tallafin man kasar ya haifar da matsalar tsadar shi.

Wannan majalisa da ake shirin rushewa ta sha alwashin mika wannan rahoton ga sabuwar majalisar da za a kafa domin binciko inda wadannan kudaden suka makale.