1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta mata kaimi ga barayin mai

Abdoulaye Mamane Amadou
August 19, 2022

A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta'azzara a Najeria, gwamnatin kasar ta ce za ta sa kafar wando guda da barayin danyen man fetur da ke wadaka da shi ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/4Fo5i
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar dai, ya ce gwamnatinsa za ta yi fito-na-fito da masu satar danyen man kasar, mako guda bayan da hukumomin Najeriyar suka cafke wata tankar dakon mai ta barauniyar hanya a gabar tekun Guinea. Shugaban ya ce ko kadan Najeriyar ba za ta amince wasu batagari su dinga amfani da dimbin arzikin danyan man fetur din da kasar ke da shi yadda suka ga dama ba, saboda hakan ya umarci jami'an gwamnatinsa da su kawo karshen wannan matsala musamman ma a yankin Niger Delta da ke Kudu maso Gabashin kasar da kuma ke da arzikin man fetur din. Najeriyar dai na da bukatar hada kai da makwabtanta domin kawo karshen  wannan matsalar cikin gaggawa, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.