1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi magana da Shugaba Buhari ta wayar tarho

September 30, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado Angela Merkel a wannan Alhamis (30.09.2021).

https://p.dw.com/p/41740
G7 Gipfel Schloss Elmau Merkel mit Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/C. Hartmann

Merkel ta kira shugaban na Najeriya ne domin nuna godiyarta ga irin kalamai na bankwana masu ratsa jiki da Shugaba Buhari ya yi mata a jawabin da ya gabatar a zauren MDD a makon da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da Femi Adesina mai taimaka wa shugaban Najeriya kan kafofin yada labarai ya fitar,  Shugaba Buhari ya jinjina wa hadin kan da Jamus ke bai wa kasashen ECOWAS. Buhari ya ce ba za a manta da gudunmawar Jamus wurin shirin farfado da Tafkin Chadi wanda zai taimaka wa kimanin mutanen yankin miliyan 30 ba. Ya kuma shaida wa Merkel cewa kasashen Afirka ba za su mance da tallafa wa 'yan gudun hijira da shugabar ta Jamus ta yi ba. 

Da ya dawo kan lamuran Najeriya, Shugaba Buhari ya shaida wa Merkel cewa kamfanonin Jamus irin su  Julius Berger da Siemens na yin aiki na gari a Najeriya. Sanarwar mahukumtan Najeriyan ta kara da cewa Angela Merkel ta yi wa Shugaba Buhari fatan alheri a kokarin da yake yi na shugabantar Najeriya mai mutane kusan miliyan 200.