1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya nemi 'yan takara da su yi murabus

Ramatu Garba Baba
May 11, 2022

Shugaba Buhari ya nemi duk masu rike da mukaman gwamnatin Najeriya da suka tsaya takara a zaben 2023 da su yi murabus nan da mako mai zuwa.

https://p.dw.com/p/4B8sw
Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

A wannan Larabar, fadar gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar inda a ciki ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga duk masu son shiga takara a zaben kasar na badi da ke rike da mukamin gwamnati, da su gaggauta yin murabus, shugaban ya nemi a mutunta wannan umarni da wa'adinsa ke cika a ranar sha shida na wannan watan Mayun 2022.

An jima ana tafka mahawara a cikin kasar kan wannan batu na son ganin ma'aikatan gwamnati musanman ministoci da suka shiga takara a zaben 2023 da ke tafe, sun soma ajiye mukaminsu tun da sun baiyana aniyarsu ta takara. A farkon shekarar 2023 miliyoyin  'yan Najeriya za su fita rumfunan zabe don kada kuri'arsu a zaben 'yan majalisu dana gwamnoni da kuma na shugaban kasar.