1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari: Akwai bukatar taimaka wa Chadi

May 25, 2021

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi imanin cewar manyan kungiyoyi da kasashe na duniya za su iya taimaka wa Chadi komawa kan tafarkin dimukaradiyya bayan mutuwar tsohon Shugaba Idriss Deby Itno.

https://p.dw.com/p/3twd8
Nigeria Katsina | Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci sa hannun manyan kungiyoyin duniya da suka hada da Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da Majalisar Dinkin Duniya, da ma kasashen Birtaniya da Faransa da kuma Amirka wajen maida kasar Chadi bisa turbar dimukaradiyya.

Shugaban ya yi wannan kiran ne yayin wani taro da shugananin wasu kasashen Afirka suka gudanar a Abuja fadar gwamnatin ta Najeriya, inda suka tattauna batutuwan siyasa da tsaro a kasashen Mali da Chadi.

Kasar Chadi dai ta kasance mai taka rawar gani wajen yaki da ta'adancin a yankin Sahel tare da tallafa wa Najeriya a yakin da take yi da 'ya'yan kungiyar Boko Haram: Sai dai mutuwar tsohon shugaban na Chadi Idris Deby na saka fargaba matuka dangane da ta'azarar lamuran tsaro a yankin Sahel.