1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Botswana ta hako lu'u-lu'u na biyu mafi girma

August 23, 2024

Kamfanin kasar Canada Lucara Diamond Corp da ya kware wajen hakar ma'adanai ya tono wani babban lu'u-lu'u da ake tunanin shi ne na biyu mafi girma da aka taba hakowa a tarihin duniya.

https://p.dw.com/p/4job1
Hoto: Monirul Bhuiyan/AFP/Getty Images

Sanarwar kamfanin ta ranar Alhamis ta ce dutsen na lu'u-lu'u mai nauyin 'carat' 2,492 an same shi ne a kasar Botswana. Bayanai sun ce tun daga shekaru kusan 120 da suka wuce da aka tono lu'u-lu'u mai nauyin 'carat' 3,106 a Afirka ta Kudu ba a sake tono lu'u-lu'u mai wannan daraja ba.

Kamfanin na Lucara ya ce ya tono ma'adanin ta amfani da fasahar zamani da ke nuna musu girman ma'adani kafin fasa dutse da suke kokarin lalubo ma'adanana kansa.

Shugaban kasar Botsawana Mokgweetsi Masisi bayan da ya karbi lu'u-lu'un a ranar Alhamis ya nuna farin cikinsa tare da daukar hoton tarihi da ma'adanin da ba a kai ga kiyasta darajarsa ba.

Ma'adanin karkashin kasa dai sune fiye da rabin kayayyakin da kasar ta Botswana ke fitar wa kasashen duniya a duk shekara.