1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da haƙar lu'u-lu'u a Zimbabwe

Sadissou YahouzaMarch 21, 2012

Zimbabwe ta bayyana cewar za ta dakatar da aikin haƙar lu'u-lu'u a ƙasar muddin gwamnati ba ta samu isassun kuɗaɗen shiga daga ma'adinin da ake cefanarwa.

https://p.dw.com/p/14Oe2
FILE -- In this Wednesday, Nov. 1, 2006 file photo miners dig for diamonds in Marange, eastern Zimbabwe. Zimbabwe's official media says the coalition government has vowed to withdraw troops from the Marange diamond fields and pledged to meet international mining standards. The report Sunday July 5, 2009 follows allegations of human rights abuses and illegal exports of "blood diamonds" from the gem-producing district in the east of the country.(AP Photo/Tsvangirayi Mukwazhi-File)
Lu'u-lu'u na daga cikin arzikin da Zimbabwe ta doga da shiHoto: AP

Ƙasar ta Zimbabuwe wadda a baya ta shara a fannin noma kuma ya kasance ƙashin bayan tattalin arziƙin ta na tsawon lokaci kafin hakan ya samu cibaya kusan shekaru goma da su ka gabata, ta samu nasarar gano ma'adanin lu'u-lu'u jibge a ƙarƙashin kasa lamarin da masu sanya idanu kan tattalin arziƙin ƙasar a ciki da wajen ƙasar ke ganin zai taimaka mata wajen farfaɗowarta daga massassarar tattalin arziƙin da ta samu kanta a ciki. Sai dai bayan wani ɗan lokaci da fara tonon ma'adanin na lu'u-lu'u, ƙasar ta Zimbabwe ba ta samu fahimtar komai daga harkar ba lamarin da ya sanya mahukuntar ƙasar fara tunanin dakatar da aikin. Ministan kuɗin ƙasar ta Zimbabwe Tandai Biti ya yi tsokaci.

Zimbabwe President Robert Mugabe, left, talks to Morgan Tsvangirai, Zimbabwe Prime Minster after the swearing in ceremony of new ministers at State House in Harare, Thursday, June, 24, 2010. (ddp images/AP Photo/Tsvangirayi Mukwazhi)
shugabab Robert Mugabe da firaminista Morgan TsvangiraiHoto: AP

"Dole ne mu samu wani abu na kirki daga lu'u-lu'u, in ba haka ba abin da za mu ke yi illa mu dinga biyan ma'aikata kudɗi wanda hakan dole zai tilasta mana mu dakatar da tononsa. Wannan ba abu ne da za mu amince da shi ba saboda abu ne mai tada hankali domin mun koma zamanin da, na kasa kula da 'yan ƙasarmu musamman ta fannin kiwon lafiya da Ilimi da samar da tituna da ma dai sauran ababan more rayuwa."

Dalilan dakatar da haƙar lu'u-lu'u a Zimbabwe

Ga alama dai ba wai mahukuntan ƙasar ta Zimbabwe ne ke nuna rashin gamsuwarsu game da wannan lamari ba, har da al'ummar ƙasar da ma dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bani adama sai dai a nasu bangare su na ganin cewar cinikin da ake yi daga lu'u-lu'un ƙasar na tafiya ne ga aljihun jam'iyyar ZANU-PF ta shuga Mugabe domin yin afmani da su wajen yaƙin neman sake zabensa a matsayin shugaban ƙasar. Baya ga wannan, al'ummar ƙasar cikida Shamiso Mtisi madugun gammayar ƙungiyoyin fararen hula na nuna damuwarsu game da adadin ƙuɗin da ake samu daga lu'u-lu'un da ake siyarwa.

"Ina ganin ko wannen ɗan kasar Zimbabwe zao so ganin lu'u-lu'un da ake hakowa na amfanarsa. gare mu wananan batu ne da ke damun mu. zai fi dacewa idan kowanne ɗan ƙasa ya san adadin ƙuɗin shigar da ake samu daga lu'u-lu'un da ake sayarwa. Idan mu ka samu waɗannan alƙaluma to ta nan ne za mu san yawan kudin da ake ba ɓangaren wutar lantarki da ruwan sha da sauran abubuwan more rauywa wanda su ka yi ƙaranci."

Yayin da al'mmar ƙasar ta Zimbabwe da ma ƙungiyoyin fararen hular ƙasar ke nuna damuwarsu dangane da batun kuɗin da ake samu daga sayar da lu'u-lu'un, ministan ma'adanan ƙasar kuma na hannun daman shugaba Mugabe wato Obert Mpofu a nasa ɓangaren cewa yai wannan ba bu ne da ya shafe su ba.

File - Miners dig for diamonds in Marange, eastern Zimbabwe, Wednesday, Nov. 1, 2006. Human Rights Watch said Friday June 26, 2009 that Zimbabwe's armed forces have taken over diamond fields in the east and killed more than 2,000 people, forcing children to search for the precious gems and beating villagers who get in the way. (ddp images/AP Photo/Tsvangirayi Mukwazhi-File)
Mata ma a barsu a baya ba wajen haƙar lu'u-lu'u.Hoto: AP

"Maganar yadda gwamnati ta samun kuɗin shiga ba abu ne da ya shalli ƙungiyoyin fararen hula ba, abin da ya kyautu su maida hankalinsu a kai shi ne kula da walwalar murtane ba wai su sanya idanu kan abin da bai shafe su ba. A iya sani na su ba kakakin ministan kuɗi ba ne... a karon farko ƙasar nan ta fara samun kuɗaɗen shiga daga lu'u-lu'un da ta ke sayarwa."

Sai dai yayin da Mr. Mfofu ke ke waɗannan kalamai, ministan kuɗin na Zimbabwe a nasa ɓangaren na dunan wannan lamari ta wata al'kiblar da ta sha ban-ban da ta takwaransa na ma'aikatar ma'adanai inda ya sake jaddada damuwarsa dangane da ƙarancin kuɗin shigar da ake samu da ma dai halin rai kwakwai-mutu kwakwai da aljihun gwamnatin ƙasar ke ciki domin a cewarsa kashi hamsin cikin ɗari kacal na ƙudodrorinsu su ke iya cimmawa.

Da ya ke maida martani game da haka, Ministan ma'adanan na Zimbabwe cewa yai, wannan ɗan tsaikon da aka samu ba zai rasa nasaba da rashin saida lu'u-lu'un ƙasar a cikin watan Janairu da na Fabrairu na wannan shekarar, to amma tunda an samu saidawa a halin yanzu ƙasar za ta samu kuɗaɗe masu Ƙauri.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal