1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHaiti

Blinken ya shawarci Haiti ta kafa gwamnatin rikon kwarya

March 8, 2024

Sakataren harkokin wajen Amurka ya bukaci a kawo wa Haiti dauki na kasa da kasa don ceto ta daga mugun halin da ta fada na rikicin 'yan daba da suka karbe iko da wasu yankuna na Port-au-Prince babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4dIIY
Haiti verlängert Ausnahmezustand
Hoto: Odelyn Joseph/AP Photo/picture alliance

A yayin tattaunawarsa da Firaministan Haiti, Antony Blinken ya bukaci Ariel Henry da ya gaggauta kafa gwamnatin mulkin rikon kwarya a matsayin mafita ga dambarwar da kasar ta fada tsawon shekaru uku.

Karin bayani: Fargabar dagulewar al'amura a Haiti

Babban jami'in diflomasiyyar na Amurka ya bukaci da a kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasar wace za ta kunshi dukannin bangarorin siyasa sannan kuma a shirya zabe cikin hanzari don dawo da Haiti kan tafarkin dimokuradiyya.

Tun bayan zaben shekarar 2016 har yanzu ba a sake gudanar da wani zabe a Haiti ba, hasali ma a halin da ake ciki kasar da ke tsibirin 'Caraïbe' ba ta da shugaban kasa da majalisar dokoki tun bayan kisan tsohon shugabanta Jovenel Moïse a shekarar 2021 watanni kalilan bayan nadin Ariel Henry da ke jagorantar kasar a yanzu a mukamin firaiminista.