1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin neman shugabanci a Haiti

Binta Aliyu Zurmi
July 19, 2021

Firaministan wucin gadi Claude Joseph zai mika mulki ga abokin karawarsa Ariel Henry.

https://p.dw.com/p/3wi2h
Claude Joseph | Interimsministerpräsident von Haiti
Hoto: Estailove St-Val/REUTERS

Ma'aikatar cikin gidan kasar Haiti ta fidda sanarwar cewa, Claude Joseph da ke rike da mukamin Firaministan kasar na wucin gadi tun bayan kisar gilla da aka yi wa shugaban kasar Jovenel Moise zai mika mulkin ga abokin karawarsa Ariel Henry da ke samun goyon bayan kasashen ketare nan ba da jimawa ba.

Ana sa ran wannan sanarwa ta kawo karshen rikicin neman shugabanci da kasar ta Haiti ke ciki, musamman ma tsakanin wadannan mutanen biyu. Ariel Henry shi ne wanda marigayi shugaba Moise ya nada firaminista, kwanaki biyu kafin kisansa da ba a kai ga rantsar da shi ba.

Kasar ta Haiti dai na fama da tarin matsaloli ko baya ga rikicin siyasa, al'ummar kasar na fama da matsanancin talauci da tsadar rayuwa.  Har kawo yanzu ana ci gaba da kame mutanen da ake tunanin suna da hannu a kisan shugaban kasar.