1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benin ta zargi Nijar da toshe kafar tattaunawa

Salissou Boukari
May 31, 2024

Shugaban kasar Benin Patrice Talon ya zargi hukumomin Nijar da toshe duk wata hanyar tataunawa ta samun mafita a takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu

https://p.dw.com/p/4gWCw
Patrice Talon na Benin da Tiani na Nijar
Patrice Talon na Benin da Tiani na NijarHoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

Shugaban kasar Benin Patrice Talon, cikin bayanin da ya yi bayan da ministansa na makamashi ya bashi rahoton ziyarar da ya kai Jamhuriyar Nijar domin samun daidaito a hakumance kan abun da ya shafi jigilar danyen mai ta bututu daga Nijar zuwa Benin duk kuwa da rufe iyaka da Nijar ta yi tsakaninta da Benin, Shugaba Talon ya nunar da cewa har yanzu hukumomin Nijar basu ba da wata fuska ba inda yake cewa:

Karin Bayani: Rikici tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin

" Ga bayanin da ministan ya yi min kan ziyararsa a Nijar ya nunar cewa bangaran Nijar basu bamu wata cikakar amsar da muke so kan wannan batu na magance harkokin danyen man da ke shigowa a kasar Benin daga Nijar ba inda suka ce sai sun sanar da hukumominsu na koli, don haka a daidai wannan lokaci ban samu wata amsa cikakkiya daga yan uwanmu na Nijar ba. Sannan Ministan yi amfani da wannan taro a Yamai ya mika wasika ta neman daidaita lamura amma shugaban na Nijar bai karbi ministar ba, kuma ina mai tabbatar muku cewa duk abin da Benin ya kamata ta yi tana yi don ganin an daidaita lamura da kasar Nijar”

Aikin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Benin
Aikin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Benin Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

A hannu daya kuma shugaban na Benin ya ce yana da yakinin cewa wannan matsala tsakaninsu da Nijar za ta kau domin su suna bin duk hanyoyin da suka dace domin ganin an kai ga hakan:

Karin Bayani: Fitar da man Nijar ta Benin cikin gagari

" Ina mai cike da fatan ganin lamura za su daidaita ba da jimawa ba tsakanin Nijar da Benin. Domin ba na ganin wasu dalillai da ke sa wa hukumomin Nijar su kafe kan bakansu na cigaba da nuna shakku ga kasar Benin. Lokacin cewa bamu yarda da juyin mulki ko kuma wani batu na takunkumi ba ya wuce ga kowa, kenan babu wasu dalillai da za su sa hukumomin Nijar a yanzu su daina ganin kimar hukumomin Benin.”

Sai dai tuni masu sharhi kan harkokin yau da kullum irin su Malam Kabirou Issa ke ganin cewa kalaman shugaban kasar Bernin zargi ne domin kuwa a fannin diflomasiyya ba haka ta kamata ya yi ba:

Karin Bayani: Benin: Martani daga 'yan kasuwar Nijar

Aikin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Benin
Aikin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Benin Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

A fuskar 'yan kasuwa ta bakin Alhaji Yacouba dan Maradi shugaban 'yan kasuwa masu shigowa da fitar da kayayaki ya ce buda iyaka tsakanin Nijar da Benin abu ne da kowa ke son gani koma da yake ya soki yadda wasu 'yan kasar ta Benin ke nemsan kaskantr da 'yan kasuwar Nijar.

Sai dai daga nashi bangare shugaban kungiyar FCR mai kula da kare hakkin jama'a da dimukuradiyya Oumarou Souley, shawara ya bayar ga shugabannin biyu da cewa su warware wannan matsala ta hanyar diflomasiyya ba tare da cece-kuce mai yawa ba.

Abun jira a gani dai shi ne matakin da shugabannin kasashen biyu za su dauka domin ganin al'umomin kasashen sun samu sauki na zirga-zirga daga wannan kasa zuwa waccan tare da komawa ga harkokin kasuwanci da mu'amnula ta yau da kullum.