1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun tsaro zai mamaye taron Faransa

Umaru AliyuMay 16, 2014

Ana ci gaba da samun ra'ayoyi masu cin karo da juna a tsakanin al'ummomin Najeriya dangane da taron da Faransa ta ɗauki nauyin shiryawa tsakanin ƙasashen yankin Sahel da Najeriya domin yaƙi da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1C1YB
Nigeria Goodluck Jonathan & Francois Hollande
Hoto: picture-alliance/dpa

An dai ɗauki shekaru ana kisan jama'a, kuma an ɗauki shekarun ana kau da ido a tsakanin Najeriya da ke fama da annobar Ƙungiyar Boko haram da kuma wasu makwabtan da ke kallon tashin hankali a matsayin barazana ga ƙasashensu.

Faransa na yunƙuri yaƙi da ta'addanci a cikin ƙasashen.

A ƙarshen makon jiya ne dai shugaban ƙasar ta Faransa Francois Hollande ya bayyana aniyarsa ta shirin taron da ya ƙunshi kasashen huɗu da ke makwabtaka da Najeriya, wanda kuma a cikinsa ake saran kammala shi da wani tsarin haɗa kai da nufin tinkarar matsalar da ke barazana ga makomar ƙasar ta Najeriya. Dr Jibrin Ibrahim da ke jagorantar ƙungiyoyi masu zaman kansu a yankin yammacin Afirka ya ce taron na iya buɗe wani sabon babi a cikin yaƙin sannan ya ƙara da cewar.

Nigeria Goodluck Jonathan, Boni Yayi & Francois Hollande
Hoto: picture-alliance/dpa

“Kasan cewar muna samun matsala da Kamaru kan batun tsaron nan, ina jin manufar haɗuwar ita ce Faransa da sauran ƙasashen, su samar da hanyoyin kawo ƙarshen tashin hankalin da ake fama da shi na Boko Haram.''

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da hirar da Ahmed Salisu ya yi da ɗaya daga cikin iyayen yaran nan, 'yan matan Chibok wanda ya so a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane