1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kama 'yan tawayen Chadi a Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa SB
April 28, 2021

A Jamhuriyar Nijar jama'a na ci gaba da dora ayar tambaya a game da dalillan kasar na kin bayyana matsayi a hakumance game da bukatar da hukumomin Chadi suka shigar a ba su hadin kai ga kamo madugun 'yan tawayen Chadi

https://p.dw.com/p/3sgko
Tschad I Militärische Operation gegen Rebellen in Ziguey
Hoto: Abdoulaye Adoum Mahamat/AA/picture alliance

A karshen makon da ya gabata ne dai a cikin watan sanarwa da ta fitar majalisar mulkin rikon kwarya ta sojojin kasar ta Chadi suka yi kira ga kasar Jamhuriyar Nijar da ta ba su hadin kai domin kamo madugun 'yan tawayen kasar ta Chadi Mahamat Mahdi Ali da sauran mayakansa  da suka gudo zuwa cikin Nijar. To sai dai har ya zuwa wannan Talata gwamnatin kasar ta Nijar ba ta fito a hakumance ta bayyana matsayinta ba a game da bukatar sabbin mahukuntan kasar ta Chadi. Hatta ma Kakakin gwamnatin Nijar Malam Tijjani abdoulkadri da na tuntuba ta wayar tarho a dazunnan ya ce ba su da wani bayani a kai. Amma kuma wasu majiyoyin tsaro masu tushe a kasar ta Nijar sun bayyana cewa kasar ta Nijar ta kama 'yan tawayen Chadin da dama tare da mika su ga hannun mahukuntan kasar. Malam Alkassoum Abdourahmane mai sharhi kann harkokin tsaro a Nijar, ya ce akwai kanshi gaskiya cikin batun kama 'yan tawayen Chadin ya kuma bayyana dalillian da ya ke suka sa gwamnatin nijar ta ki fitowa ta bayyana matsayinta a hakumance.

Afrika Tschad Konflikt Panzer in den Straßen
Hoto: REUTERS

Karin Bayani:Boren kin amincewa da gwamnatin Chadi

Sai dai duk yake cewa gwamnatin Nijar ba ta fito fili ta yi wa 'yan kasa jawabi a hakumance ba a kan ta kama ‚yan tawayen Chadin ko kuma a'a, biri na neman ya yi kama da mutum a ruwayar da ke cewa Nijar ta kama tare da mika 'yan tawayen Chadin, domin kuwa a wata wata sanarwa da kungiyar ‚yan tawayen Chadin ta fitar a jiya Litinin ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda ta ce nijar da aka dora wa nauyin shiga tsakani a cikin rikicin Chadi ya rikide zuwa ga mai goyon bayan sabbin hukumomin milkin sojan Chadin. To Amma Malam Moussa Akasar dan jarida mai binciken kokof da kuma sharhi kan harkokin tsaro a Nijar, ya ce babu dan tawayen Chadi da Nijar ta kama.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana ci gaba da yin gum da bakinta kan wannan batu na bukatar hukumomin Chadi.