1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Chadi sun nada sabon Firaiminista

Abdul-raheem Hassan MNA
April 26, 2021

Nada sabon Firaiministan na zuwa bayan da sojoji suka yi watsi da tayin tattaunawa da 'yan tawayen da suka kashe tsohon Shugaban kasar Idriss Deby a fagen daga.

https://p.dw.com/p/3sacp
Pahimi Padacke Albert | Premierminister Chad
Hoto: picture-alliance/dpa/Photoshot/Q. Benxiao

Majalisar sojojin da ke mulkin rikon kwarya a Chadi sun nada Albert Pahimi Padacke Firaiminiustan kasar. Padacke mai shekaru 54 ya taba rike mukamin Firaiminista a kasar kuma yana cikin 'yan takarar neman mukamin shugaban kasa a zaben baya-bayan nan.

Sai dai akwai fargabar cewa rashin bude kofar hawa teburin sulhu da 'yan tawayen zai tunzura su, su ci gaba da bude wuta a babban birnin kasar N'Djamena.

Wani kakakin kungiyar 'yan tawayen ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, cewa za su hade da sauran kungiyoyin 'yan bindiga da ke adawa da nada Mahamat Idriss Deby, dan marigayi Deby a mastayin shugaban riko na watanni 18 kamin shirya sabon zabe.