1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kalubalen ma su ajiya a bankuna

February 29, 2024

A wani abun da ke iya kai wa ya zuwa tasiri mai girma cikin batun kudi a Najeriya, bankunan cikin kasar na shirin rufe miliyoyin asusun ajiya sakamakon cikar wa'adin babban bankin kasar CBN na bayanan ajiya.

https://p.dw.com/p/4d2lg
Najeriya | CBN | Bankuna
Dogon layi a bankuna ba sabon abu ba ne a NajeriyaHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Duk da cewar Najeriya na da ma su asususn ajiya na bankuna kusan miliyan 150 yanzu, kasa da asusu miliyan 50 ne ke da cikakkun bayanai kasa da sa'o'i 24 da cikar wani wa'adi na babban bankin kasar CBN kan asusun ajiyar. Da ma dai an dauki lokaci ana nunin yatsa ga bankunan Najeriyar, cikin rikicin rashin tsaro da aikata laifuka a bankuna cikin kasar. Wannan wa'adi na babban bankin kasar CBN dai, ya ce duk wani asusun da ba shi da cikakkiyar rijistar bankin da ma ta dan kasa to ba zai ci gaba da samun damar hada-hadar kudi a cikinsa ba. Akalla asususn ajiya miliyan kusan 85 ne dai ake jin sabon wa'adin ka iya shafa cikin kasar da ke yi wa bankunan da ma wayoyin salula kallo da idanun mafitar aikata laifukan da suka danganci kudi da ke sauyin launi cikin kasar a halin yanzu.

Najeriya | Babban Banki | CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Tun daga tsakiyar wannan mako ne dai da ma kamfanonin sadarwar kasar suka rufe wasu layukan waya kusan miliyan 12, duk a kokarin kai karshen laifukan da ke da nasaba da kudin da ma wayoyin ke taka rawa wajen ta'azzarar su. Cikin watan Disambar shekara ta 2020 ne dai mahukuntan kasar suka nemi al'umma da su yi rijistar waya da ma asusun ajiyar tasu. Dakta Yerima Ngama dai na zaman tsohon ministan kudin kasar kuma kwararre a cikin harkar banki, kuma ya ce batun zaman lafiya a Najeriya ya wuce banki da kila ma waya ta salula. Ana dai kallon karuwar tururuwa zuwa ga bankuna a Abuja, a kokarin kaucewa toshe asusun da ke da tasiri a rayuwa da makomar miliyoyin 'yan kasar.