1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ilmantar da fursunonin Najeriya

Uwais Abubakar Idris RGB
December 28, 2021

A Najeriya fursunonin kimanin 72 ne suka samu shiga tsarin karatun digiri daga gidan yari a wani sabon tsarin shirin da jami’ar karatu daga gida ta bullo da shi a kasar.

https://p.dw.com/p/44vBF
Grenzzaun Israel Ägypten Negev Wüste
Hoto: Jim Hollander/dpa/picture alliance

Cikin wadanda za su ci gajiyar shirin, har da fursunonin biyar da ke karatun digiri na uku watau Phd, wanda sauyi ne daga tsarin da ake da shi a baya a kasar. Wadannan fursunonin da suka aikata laifuffuka iri dabam-dabam  ake tsare da su a gidan kaso, amma a wannan yanayi 72 daga cikinsu suka samu damar fara karatun digiri, biyar ke karatun digiri na uku da suka amsa ranstuwar fara karatu.

Wata dabara ce da hukumar kula da sauya halayen fursunonin da jami’ar karatu daga gida watau NOUN suka tsara, don sauya halayen fursunonin su zama mutanen kirki, ta yadda za su zamo masu amfani da kansu da ma Najeriyar.

Fursunonin 72 da yanzu suke karatun digiri dukkaninsu daga gidan yarin Kuje da ke Abuja suke karatun. Tun bayan da aka sauyawa hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya suna zuwa hukumar gyara halaye,  aka tsara hanyoyin da za’a sauya tunani da halayen na fursunonin ta yadda za su zama mutanen kirki ko bayan sun kamalla zaman gidan yari a kasar.