1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku Abubakar ya canza sheka zuwa APC

February 3, 2014

A wani abin dake iya zama cikas ga jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban Tarrayar Najeriya kuma jigo a cikin jami'iyyar ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC

https://p.dw.com/p/1B24a
Hoto: DW/K. Gänsler

Ya dai share tudu da gangare na siyasar kasar ta Najeriya don neman sa'a, kuma yace ya samo ta wajen zakara, ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da yace tazo karshe a cikin PDP tare da maida komatsansa zuwa APC ta adawa. Dama dai Atikun da ya sha gwagwarmayar neman sai an yi gyara a cikin PDP, abin da ya kai ga jagorantar tawayen farkon da ya kai ga ficewar wasu gwamnonin jam'iyyar biyar yanzu haka, kuma ke ci gaba da yi mata illa a majalisun kasar biyu. To sai dai kuma sai da yammacin ranar Lahadi ne dai Atikun da ya kamalla zagaye sassa daban daban na Najeriyar yace tura ta kai bango kuma hakuri ya kare masa cikin gidan na wadata.

“Duk manufofin da muka kafa wannan jam'iyyar da ita ba wanda ake aiwatarwa yau. An kafa kwamitin Alex Ekueme, da kuma Kwamitin Ike Nwachuku domin a gyara wannan jam'iyyar amma an ki bi, don haka jam'iyyar nan ta bar mutane, ta bar magoya bayanta, shi yasa na dauki wannan mataki”

Shegiyar uwa mai kashe 'ya'yanta ko kuma kokari na cika buri na siyasa, wannan ne dai karo na biyu da Atikun da ya taka rawa cikin harkokin PDP tun daga farkon fari ke ficewa daga lemar cikin fushi. A shekara ta 2006 dai wani rikicin cikin gida tsakaninsa da tsohon maigidansa Olusegun Obasanjo, ya kalli Atikun hada runfa da jam'iyyar can ta adawa, kafin daga baya ya sake dawowa a cikin PDP a shekara ta 2009.

To sai dai kuma sabon matakin da yazo daidai lokacin da masu Gidan Wadatar ke karade lunguna da sakunan kasar da nufin neman mafita daga dukkan alamu na iya kara baki da duhu kama daga fadar gwamantin kasar ta Aso rock in da rikicin yayi dukkan shaho, ya zuwa ga hedikwatar jam'iyyar dake takama da sabon shugaba, kuma ma suruki ga Atikun.

Vize Präsident Atiku Abubakar, Nigeria
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku AbubakarHoto: AP Photo

To sai dai kuma a fadar sabon dan APC matsalar ta wuci batu na sauya shugaban jam'iyar, ta kuma tsallaka ga tsoma bakin fadar gwamnatin kasar a cikin harkokin PDP.

“ Sau nawa. A wancan karo ma ai sabon shugabanci ne akayi aka ce za'a gyara ba gyara ba shugabancin ya tafi. Wajen shugabanci uku aka yi amma an kasa yin komai, ainihin matsalar jam'iyya shine an dauki harkokin jam'iyya da kuma mulkin kasa an damka shi wuri guda. Ba a yi mulkin jama'a ba, kuma baa iya harkar jam'iyya ba”

Raba mulki da siyasa ko kuma kokari na babakere dai, ko bayan gwamnonin, dai Atikun na zaman jami'i mafi girma da ya bar PDP dake kara kusantar zabukan tarayyar cikin halin rudani da rashin tabbas. To sai dai kuma ana kallon tasa ficewar a matsayin wani yunkuri na dana moriyar farin jini APC da ke iya bashi kafar cika burinsa na mulkar kasar ga Atikun da ya nuna kwarewa ta siyasa amma ya gaza a bisa burin mulkin kasar ta Najeriya, zargin kuma Atikun ya kira kokari na dauke hankali.

“ Zan shiga APC ne don in rayata don jama'ar Najeria baki daya, In lokacin takara kuma yazo to sai mu jira mu gani. A gaskiya bana son ku rika kawo maganar takara don sai ku dauke mana hankali daga kokari na gina jam'iyya”

Nigeria Regierungspartei PDP
Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya.....Hoto: DW/K. Gänsler

Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin PDP da nadin sabo na shugabancin ya gaza rububin sauyin shekar dake barazana ga tasirinta cikin kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu