1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yaba da matakan da Tinubu ke dauka

Abdoulaye Mamane Amadou Suleiman Babayo
January 24, 2024

Kasar Amurka ta yi alkawarin tallafa wa kasashen yankin yammacin Afirka ta fannoni da dama, ciki har da batun tsaro da karfafa dimukuradiyya, a daidai lokacin da kasashen yankin ke fama da jue-juyen mulki.

https://p.dw.com/p/4bbqr
Hoto: Evelyn Hockstein/Pool/AP/picture alliance

A yayin da yake ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya a ci gaba da wani randagin da yake wasu kasashen yammacin Afirka, babban sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yaba da matakan da gwamnatin Najeriyar ta dauka na cire tallafin man fetur, wanda ya kira cewa radadinsa ba wani mai jimawa ne ba, kana ya bayyana farin cikinsa na yunkurin Gwamnatin Tinubu na aiwatar da gagarumin bincike kan harin nan na sojan Najeriya bisa kuskure a garin Tudun Biri.

A gabanin isa a Najeriya tun daga farko Antony Blinken ya jaddada matsayar Amurka na taimaka wa kasashe masu fama da matsalolin ta'addanci yakar ayyukan 'yan ta'addan da ke ci gaba da samun gindin zama a wasu kasashen Sahel, a lokacin ganawarsu da shugaba Allassane Ouattara na kasar Côte d'ivoire.