ANC mai mulkin Afirka ta Kudu na fuskantar janyewar masoya
February 24, 2024Jam'iyya mai mulkin kasar Afirka ta Kudu ANC ta kaddamar da fara yakin neman zaben kasar da za a gudanar a ranar 29 ga Mayu mai zuwa, a daidai lokacin da kasar ke kara tsunduma cikin halin tabarbarewar tattalin arziki mafi muni a tarihinta.
Karin bayani:Julius Malema ya zargi jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu da jefa kasar cikin tasku
Shugaba Cyril Ramaphosa da jam'iyyarsa na fuskantar janyewar magoya baya da kuma bakin jini sakamakon tarin zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin iya mulki da suka yi wa gwamnatinsa katutu.
Karin bayani:Putin ya fasa halartar taron BRICS a Afirka ta Kudu
Dubban magoya bayan ANC din ne dai suka yi dafifi a filin wasa na birnin Durban, don shaida kaddamar da yakin neman zaben inda shugaba Cyril Ramaphosa ya zayyano manufofin da suka sanya a gaba don cimmawa idan sun sake samun nasarar zaben.