1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Malema ya zargi ANC da jefa kasar Afirka ta Kudu cikin tasku

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 10, 2024

Mr Malema ya zargi shugaba Cyril Ramaphosa da gurgunta harkokin tattalin arzikin kasar, da jefa jama'a cikin kuncin rayuwa, sakamakon rashin wutar lantarki da rashin aikin yi a tsakanin matasa

https://p.dw.com/p/4cGAF
Hoto: Gallo Images/IMAGO

Fitaccen mai adawa da gwamnati a kasar Afirka ta Kudu Julius Malema ya zargi jam'iyya mai mulki ta ANC da yin watsi da matsalolin da kasar ke ciki, yana mai ikirarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin ya janyo mata asarar rinjayen da take da shi a majalisar dokokin kasar a zabe mai zuwa.

Karin bayani:Mandela ya cika shekaru 10 da rasuwa

Mr Malema ya zargi shugaba Cyril Ramaphosa da gurgunta harkokin tattalin arzikin kasar, da jefa jama'a cikin kuncin rayuwa, sakamakon rashin wutar lantarki da rashin aikin yi a tsakanin matasa.

karin bayani:Israila ta yi watsi da zargin kisan kare dangi a Gaza

Ya kara da cewa za su kayar da ANC a zaben da za a gudanar a watan Mayu mai zuwa da kuma Agusta, sannan su zabi sabon shugaban kasa, yana mai alkawarta samar da aikin yi ga mutane miliyan 4 a cikin watanni 6 idan har suka samu nasarar zabe.