1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An ceto daliban sakandaren Kankara

December 18, 2020

Gwamnatin jihar katsina ta karbi Daliban makarantar sakandaren Kankara da aka sako su 344 wadanda 'yan bindiga suka yi garukuwa da su.

https://p.dw.com/p/3mvNd
Afrika Nigeria Schulkinder freigelassen
Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

Daliban dai sun kwana a jihar Zamfara bayan an karbo su daga hannun 'yan bindigar cikin dare inda mahukuntan jihar katsina suka tura motocin safa-safa aka kwaso su. Gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari shi ya karbi daliban a fadar Gwamnatin jihar.

Gwamnan na Katsina ya tausaya ma daliban inda yace shima tun da aka dauke su hankalinsa bai kwanta ba. Daga bisani ya sha alwashin ganin hakan bai kara faruwa ba gami da kira ga al'umma su ba da hadin kai wajen samar da tsaro. 

Iyaye maza da mata na cigaba da murnar dawowar yaran.