1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da mayar da martani kan jawabin Buhari

Uwais Abubakar Idris AS
October 23, 2020

Al'ummar Najeriya na cigaba da mayar da martani kan jawabin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi game da halin da kasar ta shi na tashin hankali biyo bayan zanga-zangar #EndSARS.

https://p.dw.com/p/3kM7S
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Song

Jawabin na Shugaba Buhari da ya yi ga 'yan kasar ya jawo mayar da martani musamman daga masu rajin kare demokradiyya a kan gaza fitowa fili ya yi Allah wadai da kasha-kashen da aka yi a unguwar Lekki da ke Lagos. Wannan batu dai ya fusata 'yan kasar da da dama musamman 'yan jam'iyyar adawa ta PDP.

Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Matasan Najeriya na son ganin an kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yi.Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

Su kansu matasa da suka hadu suka yi zanga-zangar suna cewa ba su gamsu da jawabin na shugaban Najeriya ba duba da gaza tabo batun kisan da suke zargin 'yansanda da aikatawa. Sai dai jmiyyar APC mai mulki a Najeriyar ta ce irin martani da ake mayarwa ba abin amincewa ba ne, domin jawabin manufarsa ita ce a samu zaman lafiya kamar yadda jigo a jam'iyyar Malam Ibrahim Masari ya bayyana.

To sai dai ga Abubakar Tsanni na kungiyar kishin kasa ta Think Nigeria ya ce jawabi muhimmi ne sai dai sulhuntawa ce mafita.
Ana dai nuna 'yar yatsa a kan zargin cewa  jami’an tsaro ne suka yi kisan, inda tuni sojin Najeriya suka musanta shiga lamarin tare da kira a jira sakamakon bincike da gwamnatin jihar Lagos ta fara.