1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi shugaban Najeriya da mallakar dukiya mai yawa

October 9, 2014

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi bazanar shigar da karan wani shafin Internet na bisa zargin Shugaba Goodluck Jonathan da mallakar dukiya mai yawa.

https://p.dw.com/p/1DSnc
Hoto: imago/Wolf P. Prange

Shi dai wannan shafi na Internet ya saka sunan Shugaba Janathan a sahu na shida, daga cikin jerin sunayen shugabannin Afirka da suka fi mallakar dukiya mai yawan gaske, inda shafin ya ce shugaban na Najeriya na da milyan 100 na dalar Amirka.

Sai dai da take mayar da martani kan wannan batu, fadar shugaban kasar ta Najeriya, ta ce Shugaba Jonathan dai bai taba zama wani dan kasuwa, kowani dan kwangila ba har inda zai mallaki wadannan kudade. Hakan dai na nufin cewa shugaban ya samu wadannan kudade ne ba ta hanyar gaskiya ba tun lokacin da ya kama mulki a shekara ta 2010, abin da fadar shugaban na Najeriya ta karyata, tare da neman wannan shafi da ya karyata wannan batu ko kuma su fuskanci shari'a.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo