SiyasaTurai
An yi gwanjon agogon zinare na attajirin jirgin Titanic
April 28, 2024Talla
Iyalan marigayi John Jacob Astor IV sun yi gwanjon agogon akan Euro milyan 1.38 kwatankwacin Dalar Amurka milyan 1.46, wanda daga bisani wani Ba'Amurke ya sayi agogon.
Karin bayani: Mutanen da ke cikin jirgin da ya bata a teku sun mutu
Astor ya yi nasarar kubutar da matarsa Mai dauke da juna biyu daga cikin jirgin ruwan na Titanic, kafin daga bisa ya mutu a cikin jirgin da ya yi hadari a watan Afrilun 1912 kimanin shekaru 112.
Karin bayani: Attajirai biyar sun nuste a teku
Masu gwanjon kayan tarihin jirgin na Titanic sun ce agogon ya kasance abu mafi tsada da aka sayar daga cikin tarkacen jirgin, baya ga sarewar da aka yi amfani da ita wajen nishadantar da fasinjojin jirgin na Titanic da aka sayar akan fam milyan 1.1 a 2013.