1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ji duriyar mutanen da suka bace a kusa da jirgin Titanic

June 21, 2023

Masu gadin gabar ruwan Amirka sun ce sun jiyo duriyar mutanen nan biyar da jirgin karkashin ruwansu ya nutse a lokacin da suke kokarin zuwa gurin gawar jirgin ruwan Titanic.

https://p.dw.com/p/4StDL
Titan | Tauchboot bei Tauchgang zur Titanic vermisst
Hoto: OceanGate Expeditions/dpa/picture alliance

Kwanaki hudu bayan nutsewar jirgin karkashin ruwan tawagar mutum biyar masu kokarin zuwa ganin makeken jirgin ruwan nan na Titanic da ya yi hadari yau da shekaru 111 a Tekun Atlantic, a wannan Laraba masu gadin gabar ruwan Amirka sun ce sun jiyo duriyar mutanen.

Jim kadan bayan sanar da wannan labari, jami'an ceton kasar Kanada bisa jagoranci takwarorinsu na Amirka sun kara samun kwarin gwiwa, inda tuni suka sake bazama domin ceto mutanen biyar kafin gobe Alhamis.

Makeken jirgin ruwan Titanic mafi girma a lokacin da ya fara aiki, ya yi hatsari ne a shekarar 1912 a Tekun Atlantic yayin da yake kan haryarsa daga Southampton izuwa birnin New York na Amirka.  Daga wannan lokaci ne dai hamshaken masu kudi ke zuwa yawon bude ido a kusa da gawar jirgin wacce ke a zurfin mita 4.000 a karshin Tekun Atlantic kwatankwacin kilomita hudu ke nan.

Yayin da Shugaba Joe Biden na Amirka ya samu wannan labari, ya karkafa fatan za a ci gaba da lalube don ceto mutanen biyar da suka hadar da wani hamshakin attajiri dan kasar Burtaniya, da dan Amirka guda da dan faransa guda da kuma mutane biyu 'yan kasar Paskistan.