1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara a Zamfara sun yi garkuwa da mutane 20

Abdoulaye Mamane Amadou
August 16, 2021

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya sun ce 'yan bindiga sun kai hari a kwalejin koyon aikin gona ta jihar tare da hallaka mutane uku.

https://p.dw.com/p/3z34C
Nigeria Hunderte Mädchen in Zamfara entführt
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Bayan kisan 'yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutun 20 ciki har da daliban makarantar 15 a cewar Abdullahi Aminu daya daga shuwagabannin makarantar a yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP. Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce akalla dalibai 1000 ne aka yi garkuwa da su a sassan jihohin Najeriya dabam-daban tun daga watan Disanban bara zauke yanzu, kana kuma galibin wadanda aka sakin sun kubuta ne bayan an biya kudin fansa, ko da ya ke har yanzu 'yan bindigar da ke addabar yankin na cigaba da garkuwa da wasunsu da dama.