An samu daya daga cikin 'yan matan Chibok
May 18, 2016Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewa an samu daya daga cikin 'yan mata 'yan makaranta na Chibok wadanda tsagerun kungiyar Boko Haram suka sace fiye da shekaru biyu da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito 'yan gwagwarmya da shugaban al'umma suna tabbatar da labarin. Fiye da shekaru biyu da suka gabata aka sace 'yan mata fiye da 200 a garin Chibok na Jihar Borno da ke yabnkin arewa maso gabashin Najeriya, inda tsagerun na Boko Haram suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.