1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An rantsar da Ching-te a matsayin sabon shugaban Taiwan

May 20, 2024

Rahotanni daga birnin Taipei na cewa duk da matsin lamba daga hukumomin Chaina, an rantsar da Lai Ching-te na jam'iyyar Democratic Progressive Party (DPP) a matsayin sabon shugaban tsibirin Taiwan.

https://p.dw.com/p/4g3sO
Shugabar Taiwan mai barin gado (daga hagu) Tsai Ing-wen, da sabon shugaban yankin Lai Ching-te (daga dama) a yayin bikin rantsuwar kama aiki
Shugabar Taiwan mai barin gado (daga hagu) Tsai Ing-wen, da sabon shugaban yankin Lai Ching-te (daga dama) a yayin bikin rantsuwar kama aikiHoto: Sam Yeh/AFP/Getty Images

Ma'aikatar harkokin wajen Taiwan ta sanar da cewa sama da baki 500 da wakilan kasashen duniya 51 da shugabannin kasashen duniya 5 wadanda ke da huldar diflomasiyya da Taiwan ne suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban tsibirin a wannan rana ta litinin 20 ga watan Mayun 2024.

Karin bayani: Taiwan: Al'umma na kada kuri'a

Lai dan shekara 64, shi ne zai ja ragamar tsabirin na Taiwan da ke da kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai tun daga 1949, wanda kasar Chaina ke ikirarin cewa mallakinta ne. Kazalika a dai wannan rana an rantsar da jakadiyar Taiwan a Amurka Hsiao Bi-khim 'yar shekara 52 a matsayin mataimakiyar shugabar kasar.