An nada sabon sarkin Dutse da ke Jaigawa
February 5, 2023Talla
Kwanaki biyar bayan rasuwar Sarkin Dutse mai martaba Nuhu Muhammad Sunusi, gwamnan Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya amince da nadin Hamim Muhammad Nuhu Sunusi da ga marigayin a matsayin sabon sarki Dutse a jihar Jigawa, kamar yadda wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta tabbatar wa wakiliyarmu a Jigawa Zainab Shu'aibu Rabo.
Hameem mai shekaru 42 a duniya, zai kasance sarki na 19 a jerin sarakunan Fulani kuma sarki mai daraja ta 1 a jihar Jigawa. Ya samu rinjayen kuri'un wadanda suke zaban sarki kafin gwamnan jihar Jagawa ya tabbatar da nadin sabon sarkin