1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya rantsar da sabon alkalin alkalai

Ubale Musa AMA(Lateefa)
June 27, 2022

Bayan shafe dogon lokaci ana kila wa kala, daga karshe babban alkalin Najeriya mai shari'a Ibrahim Tanko Mohammed ya ajiye aikinsa, inda aka nada Justice Olukayode Oriwoola.

https://p.dw.com/p/4DKCJ
Mai shara'a Olukayode Oriwoola alkalin alkalai na Najeriya
Mai shara'a Olukayode Oriwoola alkalin alkalai na NajeriyaHoto: Alli Tolani ©2020

A wani biki da ya samu halartar jami'an gwamnatin da manyan alkalai na Najeriya da a ciki aka rantsar da sabon alkalin alkalai, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi sashen shari'ar Najeriya da ya kaucewa yin duk wani abun da zai iya kaiwa ga yan kasar dawowa daga rakiyar kimarsa. Shugaba Buhari ya ce "Najeriya na tunkarar babban zabe mai tasiri a shekarar 2023, kada alkalai su sake suyi wani abun da zai zubar musu da mutunci da kima a idon 'yan Najeriya."  Mai shari'a Ariwoola na shirin daukar bangaren shari'ar dake cikin rudani bayan da a cikin yanayi na ba zato ba tsammani, babban alkalin Najeriya ya baiyana ajiye aikinsa, ko da yake an ambaci batun rashin lafiya daga cikin hujjar saukar mai shari'a Ibrahim Tanko Mohammed daga matsayin da ke zama na biyar cikin jerin masu rike da madafan iko a gwamnatin Najeriya.

Karin Bayani: Najeriya alkalin alkalai ya yi murabus

A shekara ta 2019 ne Tanko Mohammed ya zama babban alkalin kasar bayan rikicin da ya mamaye tsohon babban alkalin Najeriya mai shari'a Walter Onoghen, tun bayan da zama alkalin kotun koli ta kasar a shekarar ta 2005. Mai shekaru 68 a duniya, ana yi wa Tanko Mohammed kallon mai saukin kai da kokarin bin dokokin shari'a, ko da yake daga baya bayan nan tankon ya fuskanci turjiyar cikin gida a kotun kolin, inda wasu alkalai 14 suka rubuta wata wasikar da a cikinta suka yi korafi na lalacewar lamura a cikin yanayin kotun, suna masu zargin cin hanci da rashuwa da ke neman mamaye harkokin shari'ar kotun. 

Harabar kotun kolin Najeriya Abuja
Harabar kotun kolin Najeriya AbujaHoto: U.A. Idris

Barrister Saidu Mohammed Tudun Wada lauya mai zaman kansa a Najeriya yace tanko ya yi rawar gani wajen kara yawan manyan lauyoyi. "Mutum ne mai kaffa-kaffa, kuma mai son yin adalci, mu lauyoyi muna tunawa da shi a matsayin mutumin da ya fadada samun manyan lauyoyi daga 10 zuwa 88 kamar yadda aka gani."

Karin Bayani: Bai wa kananan hukumomi 'yanci a Najeriya

Duk da cewar babu wani zargin da ake ta'allakawa a kai tsaye da alkalin dake barin gado, Tanko Mohammed na zaman babban alkalin kotun kolin na biyu dake yar da kwallon mangoro da nufin kila hutawa da kuda cikin babbar kotun mafi tasiri. Kafin shi kuma wanda ya gada Walter Onoghen, yaji har a ka sakamakon zargin gaza aiyyana dukiyarsa ga hukumar da'ar ma'aikata ta kasa. Barrister Buhari Yusuf cewa ya yi. "Ana ganin shi ne sananne ne ga alkalai kuma yana da digirin-digirgir kan abun d aya shafi shari'a. Yana da kwarewa, ta fito da wa da wani salo na sakarwa alkalai mara suyi abun da suke so." Tuni aka nada wani sabon babban alkalin kotun na najeriya a farkon wannan makon