1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kubutar da sojan da aka sace a Kaduna

September 18, 2021

Sojoji a Najeriya sun kubutar da wani hafsansu da 'yan bindiga suka sace shi makonni uku da suka gabata, a kwalejin horar da manyan hafsoshi ta NDA da ke a Kaduna.

https://p.dw.com/p/40UfY
Symbolbild Nigeria Armee
Hoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

A ranar 24 ga watan na jiya ne 'yan bindigar suka kada hantar hukumomi da sauran 'yan Najeriya, inda suka shiga kwalejin horar da manyan hafsoshi na NDA da ke a Kaduna inda suka kashe sojoji biyu tare da awon gaba da daya.

A ranar Juma'a ne sojojin  Najeriyar suka kai hari a maboyar 'yan bindigar wanda ke yankin Afaka, 'yar tazara da kwalejin na NDA inda suke rike da jami'in da suka sace.

Sanarwar sojojin ta ce an yi musayar wuta tsakanin dakarun da 'yan bindigar kafin daga bisani suka ci karfin su; kuma suka kwato jami'in nasu.

Sojojin sun kuma ce sun yi nasarar kashe 'yan bindigar da dama a artabun.