1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An kubutar da mutum kimanin 500

Ramatu Garba Baba
October 16, 2019

A karo na biyu a mako guda kenan da 'yan sanda ke kubutar da maza da kananan yara daga makarantun Islamiya a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3RP7u
Nigeria Polizei befreit Koranschüler aus unmenschlichen Bedingungen
Hoto: Reuters/Str

'Yan sandan jihar da suka kai samame makarantar, sun ce sun kubutar da maza da yara masu kananan shekaru da ake daure dasu da mari ko sarka, wasu daga cikinsu, sun shedawa musu halin da suka kasance na tsananin azaba tun bayan da suka sami kansu a makarantar.

Wannan na zuwa ne kwana guda da kubutar da wasu mutum saba'in 'yan shekara tsakanin bakwai zuwa arba'in a wata makarantar Islamiya da ke garin Daura a jihar ta Katsina. Kawo yanzu mutum dubu daya aka kubutar daga ire-iren wadannan makarantu da iyaye ke kai yara kangararu don gyara musu tarbiya a yankin Arewacin Najeriya.

Bayan samamen na Daura da ya kasance mahaifar Shugaban kasar,  ya soma fuskantar matsin lamba kan daukar matakin gaggawa don gano dubbai yaran da ake zaton na watse a wasu makarantun a Najeriyan.