1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kona ofishin INEC a kudancin Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
November 28, 2022

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewar hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce an kona wani ofishinta da kayayakin zabe da dama a kudu maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/4KBjB
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Mai magana da yawun hukumar Festus Okoye ya ce lamarin ya auku a jiya Lahadi a yanki Izza da ke jihar Ebonyi inda wasu da ba a kai ga sanin ko su waye ba suka cinna wa ofishin INEC din wuta ya kuma kone kurmus.

Mista Okoye ya ce babu wani jami'insu da abun ya rutsa da shi sai dai sun yi asarar kayayakin da suka hada da akwatunan zabe 340 da runfunan zabe 130 da janaraton samar da wuta 14 da kuma katunan zabe da dama.

Wannan shi ne karo na uku a tsukin makwanni uku da ake kona ofishin hukumar zaben a wasu sassan kasar.

Duk da dai babu wanda ya dauki alhakin wannan aika-aikan, kudancin Najeriya na fuskantar ayyukan yan kungiyar IPOB da ke rajin ballewa daga kasar.